IQNA

Hana Gudanar Da Tarukan Ashura A kasar Bahrain

21:57 - October 03, 2016
Lambar Labari: 3480821
Bangaren kasa da kasa, mai kula da harokin kare hakkin al’ummar Bahraina yankin turai ya bayyana hana gudanar da sallar Juma’a akasar da kuma tarukan a Ashura a matsayin babban zalunci.
Kamfamin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Manama Post cewa, Ahma Saffar b mai kula da harokin kare hakkin al’ummar Bahraina yankin kasashen nahiyar turai ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, daga cikin zaluncin mahukuntan Bahrain tun daga shekara ta 2011 shi ne hana gudanar da sallar Juma’a a kasar da kuma tarukan a Ashura a kasar.

A cikin bayanin nasa ya kara da cewa dole ne mahukuntan Bahrain su kwana da sanin cewa kasar ba mallakinsu b ace, mallakin al’ummar kasar ce baki daya, saboda haka baya halasta gare su su gudanar da tarukan addini da mafi yawan al’ummar kasar suke gudanarwa.

Haka nan kuma ya kirayi masana da kuma masu kare hakkokin yan adama koina cikin fadin duniya da su sake nauyin da kensu na bayyana wa duniya abin da yake faruwa a kasar Bahrain na zaluncin da al’ummar kasar ke fyskanta.

Kamar yadda kuma bayyana cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin ganin an gabatar da wannan batua gaban kotun manyan laifuka ta duniya domin hukunta azzalumai daga cikin masu mulkin kama karya kan al’ummar kasar Bahrain.

Daga karshe ya bayyana bin dayake faruwa kan al’ummar wannan kasa da cewa yana daga cikin nauoin zaluncin da duniya take shedawa a cikin wanan karni.

3535073


captcha