IQNA

Darul Ifta A Masar Bai Amince Da Kiran Daesh Da Daular Musulunci Ba

23:30 - October 05, 2016
Lambar Labari: 3480826
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa na kasar masar ya bayyana cewa ba su amince da kiran ‘yan ta’addan Daesh da daular muslunci da ake yi ba.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar alalam cewa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa ba za su taba amince da kiran ‘yan ta’addan Daesh da kalamar daular muslunci da wasu kafofin yada labarai suke yi ba a wasu kasashen duniya.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanataa da wata tashar talabijin a kasar ta masar, inda ya bayyana cewa babu abin da ya hada addinin muslunci da abin da ‘yan ta’addan daesh ke yi, a kan haka kiran wannan kungiya da daular muslunci da kuma ci gaba da yada hakan, wani salo ne na neman a bata sunan musulunci.

Shauki Allam ya kara da cewa wani sabon bincike da aka gudanar a cikin kasar ta Masar ya nuna cewa, mafi yawan mambobin kungiyar ta’addanci ta daesh ba su san komai dangane da addinin muslunci ba, in banda tsaurin kai da da rashin kunya da jahilci.

Wannan martini da malamain ya mayar dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu kafofin yada labarai na kasashen turai suke ta yin amfani da wannan kalma ta daular muslunc suna nufin kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS.

Akidar wahabiyanci dai ita ce babban tushe na akidar ta’addanci da ke haifar da kungiyoyin yan ta’adda da sunaye daban-daban da suke bata sunann addinin muslunci a duniya, suna kasha musulmi da wand aba musulmi ba, bil hasali ba akasarin wadanda suka fi kashewa musulmi ne.

3535295



captcha