IQNA

Matakan Kiyayya Da Mazhabar Shi’a A Masar

23:21 - October 11, 2016
Lambar Labari: 3480847
Bangaren kasa da kasa, a wani mataki na takura mabiya mazhabar shi’a a Masar jami’an tsaro sun dauki matakin hana taron Ashura a masallacin Imam Hussain (AS) da Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mubashir Misr cewa, jami’an tsaro a cikin kayan sarki sun dauki matakan hana isa masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkahira.

Jami’an tsaron sun dauki wannan matakin ne tun a daren jiya domin hana gdanar da duk wani taro na juyayin Ashura da aka saba gudanarwa a wurin tsawon daruruwan shekaru.

Jami’an tsaron baya ga rufe hanyoyin isa wurin, sun kuma dauki matakin ganin cewa bas u bari an gudanar da irin wadannan taruka ba kamar yadda aka saba saboda dalilan da ba su bayyana ba.

Wannan lamari dai bai zo ma kowa da mamaki ba, idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin kama karya ta kasar Masar take yin biyayya ga masarautar da ke daukar nauyinta tare da ba ta kudaden shiga, wadda ke kan gaba wajen kiyayya da mazhabar iyalan gidan manzon Allah a duniya.

3537295


captcha