Wannan mataki dai ya zo a cikin kwanakin farko na watan muharram a wanda a cikin su mabiya mazhaba iyalan gidan manzo ke gudanar da taruka har zuwa ranar goma ga watan.
A cikin masalalcin Imam Hussain akwai wani bangare da ake cewa nan ne aka bizne kan Imam Hussain (AS) a lokacin da makiya manzon Allah suka kasha shi.
Tun kafin wannan lokacin dai masu dauke da akidar wahabiyanci da kafirta musulmi sun ta kai komo domin ganin an hana mabiya mazhabar shia gudanar da tarukansu da suka saba yi tsawon daruruwan shekaru a wurin.