Abin ya faru jiya a majalisar dinkin duniya babban abin kunya ne, inda jakadan haramtcciyar kasar Isra'ila ya mike yana bayyana cewa an yi barazanar kisa ne akan shugabar UNESCO har ta bayyana cewa masallacin aqsa mallakin msuulmi ne.
Hukumar ta gabatar da wani daftrin kudiri da ke nuna cewa masallacin aqsa na msuulmi, kuma an kada kuri'a kan wannan daftarin kudiri, inda kasashe 58 suka kada kuri'a, wasu 24 sun amince, wasu 6 kuma suka amincewa yayin da 26 suka ki kada kuri'a sai kuma wasu da bas u uffan ba.
Wannan ya zama wata babbar nasara ga al'ummar palastinu da kuma musulmi baki daya, wanda ya tabbatar da cewa su ne suke da hakkin kuma su ne ake zalunta a kan idanun duniya.