Kwamitin kula da shirya tarukan addini na kasar Senegal ne ya dauki nauyin shirya taron a yankin Magal, tare da halartar malamai da masana daga kasashe 10 na duniya.
Babban sakataren cibiyar Ahlul bait (AS) Hojjatol Islam Akhtari ya samu gayyata zuwa halartar taron daga shugaban darikar Muridiyyah a kasar, inda ya gabatar da jawabi tare da bayyana mahangar jagoran juyin Islama a wurin.
Daga cikin abubuwan da ya bayyana kuwa, har da yadda jagora yake ganin wajabcin zaman musulmi cikin fadaka, domin fuskatar muhimman lamurran da ke a gabansu, tare da sanin cewa babban abin da ke gabansu shi ne hada kai da juna, domin makiya muslunci babu ruwansu d wani banbancin fahimta atsakanin msuulmi, dukkanin musulmi makiya ne a wurinsu.
Musamman ma yadda Amurkatake ta hankoron ganin ta yi amfani da wasu daga shugabannin musulmin da sarakunan larabawa wajen aiwatar da wannan mummunar manufa tata akan musulmi, tare da rusa kasashensu da haifar da kungiyoyin yan ta’adda da sunan addini ko skare sunna, domin a bata musulunci a idon duniya, wanda kuma shi ne abin da yake faruwa yanzu.