Babbar manufar bude wannan makaranta a cewar jakadan ita ce, kara karfafa lamarin hardar kur’ani mai tsarki ga yaran maa’akata yan kasashen ketare, da kuma koyar da su harshen turanci da lissafi da wasu ilmomi na al’adun muslunci.
Ya kara da cewa wannan makaranta za ta ci gaba da kasancewa ne a karkashin bangaren kula da harkokin al’adu na jami’ar Iskandariyya.
An dai gina wannan makaranta da nufin kara karfafa harkokin addinine ga yaran jami’an diplomasiyya da sauran yan kasashen ketare, kuma cewarsa yayan ma’aikatan Malaysia da ke Iskandariyya za su biya kashi 30 ne cikin dari kawai.
Shi ma a nasa bangaren Adlad Muhammad Shakik mataimakin jakadan kasar ta Malaysia Masar ya halarci tare da wasu jami’ar huldar diplomasiyya na kasar.