IQNA

23:49 - November 02, 2016
Lambar Labari: 3480902
Bangaren kasa da kasa, Rajio Chandraskar wani dan majalisar dokokin kasar India ya bukaci ministan harkokin cikin gida ya hana yaduwar akidar ta’addanci da sunan addini bisa salo irin na Saudiyyah.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Indian 364 cewa, Rajio Chandraskar wani dan majalisar dokokin kasar India ya bukaci ministan harkokin cikin gida ya hana yaduwar akidar ta’addanci da sunan addini bisa salo irin na Saudiyyah wato wahabiyanci kokuma salafiyanci.

Ya ci gaba da cewa irin wadannan mutanen suna karbar makudan kudade daga kasar saudiyya, wasu suna shigowa da sunan yan kasuwa masu saka hannyaen jari, inda sukan nufi irin masallatan mutanen da ke dauke da akidarsu suna ajiye musu makudan kudi, wanda hakan kuma yana da hadari bisa ga abin da ak gani na yada akidar da ke kai ga haifar da ta’addanci da sunan yada muslunci.

Dan majalisar ya kara da cewa, dan gwamnati ba ta dauki matakan da suka dace ba wata takawa salafawa birki da ke karbar kudi daga Saudiyya ba, to India za ta zama cikin kasashen da ske fuskantar barazanar ta’addanci, inda ya danganta hakan da abin da ya faru a Keshmir.

3542850


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: