IQNA

21:32 - November 26, 2016
Lambar Labari: 3480975
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani taron baje koli na kur'ani mai tsarki a dakin karato na Hampton da ke birnin malborn a a jahar Victoria ta Australia.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Herald Sun cewa, wannan shi en karo na biyu da ake gudanar da irin wannan baje koli na kur'ani mai tsarki.

Babbar manufar gudanar da wannan baje koli dai ita ce bayyana hakinanin koyarwa ta kur'ani mai tsarki, sabann irin yadda ake yada mummunar fusa dangane da addinin muslunci da kuma kur'ani mai tsarki.

Kasar dai tana daga cikin kasashen da musulmi kan yawaita yin hijia zuwa cikinta, amma daga bisani sakamakon bullar ayyukan masu akidar kafirta muuslmi da kuma ayyukan ta'addancin da suke gudanarwa da sunan muslunci, hakan ya bata sunan mulsunci matuka a wurin mutanen kasar Australia.

Wannan ne ya sanya masana daga cikin musulmi da suke zaune a kasar mikewa wajen ganin sun wayar da kan al'ummar kasar dangane da musulunci da kuma hakikanin koyarwarsa, da kuma banbancin muslunci na gaskiya da kuma 'yan ta'adda, kuma ga dukkanin alamu hakan yana yin tasiri.

3549124


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، baje koli ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: