IQNA

23:48 - November 27, 2016
Lambar Labari: 3480978
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taron tunawa da wafartin manzon Allah (SAW) a mcibiyar Imam Ali (AS) a birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden.

Kamfanin diloalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na imamalicenter.se cewa, an fara gudanar da wannan a ranar 28 ga watan safar ranar wafatin manzon Allah (SAW) da kuma shahadar Imam Hassan Mujtaba (AS) wanda zai ci gaba har zuwa 30 ga watan ranar shahadar Imam Ridha (AS).

Babbr manufar taron dai it ace tunawa da wadnnan bayin Allah manyan jiga-jigan addini, wadanda su ne suke a matsayin fitilun addini, kama daga shi kansa manzon Allah wanda shi ne babbar filar haske ta muslucni da kuma iyalan gidan limaman shirya amincin Allah ya tabbata a gare su.

Za a ci gaba da gabatar da jawabai da kuma wakoki na alhinin wafatin manzon Allah (SAW) da kuma shahadar Imamai biyu masu tsarki a cibiyar ta Imam Ali (AS) da ke birnin na Stockholm.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gdanar da irin wadannan taruka masu albarka a wannan cibiya ba, kamar yadda aka saba malamai da kuma masu bege da ke wakokin alhini duk suna halarta.

Haka nan kuma masoya mnzon Allah da iyalan gidansa tsarka da suka hada da ‘yan shi’a da ma wasu sauran musulmi duk suna halartar wannan zaman taro mai albarka kamar kowace shekara.

3549488


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: