IQNA

Tarukan Maulidin Manzon Allah (SAW) A Kasar Canada

22:34 - December 09, 2016
Lambar Labari: 3481017
Bangaren kasa da kasa, musulmi mazauna yankin Bil da ke cikin gundumar Antarioa kasar Canada suna shirin fara gudanar da maulidin manzon Allah (SAW).

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na SAFocus cewa, kwamitin musulmi yan sunna na yankin Bil suna shirin fara gudanar da maulidin manzon Allah (SAW)

Bisa ga al’ada ana fudanar da tarukan maulidin ne daga rana ta sha ta watan maulidi, har zuwa rana ta goma sha tara, wanda kuma dukkanin bangarorin na musulmi suna shiga cikin wadannan trauka masu albarka, in banda masu akidar kafirta musulmi da suke ganin hakan baya halasta.

Jami’ar Almustafa da wasu daga cikin kngiyoyin yan kasar Pakistan suna shirin gudanar da wani babban taron na maulidin namnzon Allah a cikin mako mai zuwa a cikin yankin na Antorio, wanda aka gayyaci dukkanin bangarori musulmi domin halarta.

Musulmi suna gudanar da wani kamfe a daidai wannan lokaci mai albarka na haihuwar fiyayyen halitta a kasar ta Canada, inda suke bayar da furanni ga mutane musamman ma wadanda ba musulmi, domin isar musu da sakon ‘yan adamtaka da girma dan adam da son zaman lafiya da musulunci ya koyar da musulmi.

3552151


captcha