Wannan shiri ya kunshi dukkanin musulmia duk inda suke a duniya za su iya shiga cikinsa, domin ta hanyar yanar gizo ne, kuma ana koyar da hardar kur'ani da kuma karatu, kamar yadda aka samar da ajujuwa na mutane da shekaru daban-daban.
Daga cikin ajujuwan akwai na wadanda suka riga suka fara karatun, kuma suna ci gaba, kamar yadda kuma wadanda sun kebanci wadanda suka fara ne tun daga farko.
Daga lokacin da mutum ya yi rijistar sunasa akwai malami na musamman wanda zai dauki nauyin kula da karatunsa ko kuma hardarsa a aji na musamman, wanda ya yi daidai da matsayinsa na harda ko karatu.
Ga wadanda suke son karin bayani kan yadda wannan shiri yake gudana, za su iya tuntuba ta hanyar wannan adireshi na email kamar haka «info@iou.edu.gm ».
Kimanin kashi 95 na mutanen kasar Gambia miliyan daya da dubu 800 musulmi, kuma kasar it ace kasa ta biyu bayan Mauritaniya da ake kira jamhuriyar muslunci a cikin nahiyar afirka.