Rahoton ya ce jami'an tsaron sun yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu taron murnar maulidin manzon Allah (SAW) a yankin Diraz da wasu yankuna da dama na kasar, tare da keta tutoci da suke dauke da rubuce-rubuce na yabon manzon Allah da aka kafa a wuraren.
Abin tuni a nan dai shi ne, fiye da kashi 86% na al'ummar kasar Bahrain dai mabiya mazhabar shi'a ne, yayin da masarautar kasar wadda 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka kafa, take bin tafarkin akidar wahabiyanci, sauran al'ummar kasar kuma sun hada da 'yan sunnah da kuma Abadiyyah da kiristoci.