IQNA

Marubucin Kur’ani Dan Kasar Oman Ya Rasu

23:49 - December 20, 2016
Lambar Labari: 3481052
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne Allah ya yi Salim Bin Khalfan Albaluchi dan kasar Oman rasuwa, wanda ya share shekaru 12 yana hidima ga kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na «atheer.om» cewa, Salin Bin khalfan Baluchi ya rubuta kur’ani na farko da hannunsa ne a cikin ta 1424 hijira kamariyya, ya kuma kwashe shekaru 12 yana rubuta kur’ani mai tsarki da hannunsa.

Wannan kur’ani wanda yake kallonsa amatsayin aikinsa mafi muhimanci a rayuwarsa, ya rubuta shi ne ta hanyar yin amfani da abubuwa dsa dama makima da ya hada tawada da su, kamar yadda kuma ya yi amfani da ruwan azurfa wanda aka yio amfani da shi a wajen bayan littafin.

Kamar yadda kuma nauyinsa ya kai kilo 25 haka nan kuma shafukansa sun kai 604, wanda ya zama daya daga cikin abubuwa na tarihi a kasar Oman da za a rika tunawa da shi ana alfahari da shi, sakamakon wannan gagarumin aiki da ya yi a fagen yada ilimin kur’ani mai tsarki.

Malamin wanda aka haifa a shhekara ta 1960 ya kasance a sahun gaba wajen koyar da ilmin kur’ani mai tsarki ga dalibai a kasar ta Oman.

A cikin shekara ta 1992 ne ya fara koyar da rubutun kur’ani da kuma yadda ake kayata kur’ani mai tsarki wajen rubutunsa da saka alamomi, da kuma fitar da surori, wanda kuma ya rubuta littafi a kan wannan ilimi da ake amfani da shi a makarantun kur’ani a kasar a halin yanzu.

3555263


captcha