Shugaban kasar ta Aljeriya Abdulazizi Butaflika wanda bai samu halartar bude taron ba, ya aike da wakilinsa kuma babban mai ba shi shawara kan harkokin addini Muhammad Ali Bu Ghazi, wanda ya karanta jawabin shugaban kasar a gaban mahalarta taron.
A cikin bayanin nasa, shugaba Butaflika ya bayyana muhimamncin gudanar da irin wadannan taruka, domin wayar da kan al'umma dangane da muhimamncin koyarwar kur'ani ga musulmi, da kuma yadda kur'ani mai tsarki yake koyar da musulmi yin aiki da hankali a kowane lokaci, da kuma kyawawan dabiu da zaman lafiya tare da sauran al'ummomi.
Ya kara da cewa babbar matsalar da msuulmi suka shiga ciki a halin yanzu ta samo asali ne da rashin yin riko da koyarwar da ke cikin kur'ani mai tsarki, kamar yadda kuma a daya bangaren wasu masu mummuanr akida suke yin amfani da kur'ani wajen aikata ta'addanci, wanda hakan ke bata sunan kur'ani da kuma musuluncin baki daya aidon duniya.
Wannan taro dai zai ci gaba da guda har tsawon mako guda a nan gaba, inda malamai da masana za su ci gaba da gabatar da bayanai da kuam kasidu, wadanda daga bisani za a wallafa su a littafi guda daya.