IQNA

An Kona Tutar Isra’ila A Kasar Bahrain

20:02 - December 30, 2016
Lambar Labari: 3481084
Bangaren kasa da kasa, dubban mutanen kasar Bahrain ne suka gudanar da gangami a unguwar Diraz da ke gefen birnin Manama, domin yin Allawadai da ziyarar tawagar Isra’ila a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, dubban mutanen sun taru ne a kofar gidan babban malamin addinin muslunci na kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim.

Masu gangamin sun yi ta rera take yin Allawadai da masarautar Alkhalifah, kan yadda ta tarbi tawagar yahudawan sahyuniya daga Isra’ila, tare da bude sabon shafin kyakkayawar alaka a bayyane tare da Isra’ila, wanda hakan yake a mtsayin cin zarafin ga dukkanin al’ummar kasar Bahrain, wadanda ba su amince da hakan ba.

Haka nan kuma masu gangamin sun kona tutar haratacciyar kasar Isra’ila a wurin, a wata alama da ke cewa kulla alaka tsakanin Bahrain da Isra’ila da ba yawun al’ummar kasar ne ba.

Masarautar Bahrain dai na daga cikin masarautun larabawa da suke da kyakkyawar alaka da Isra’ila a boye, inda Isra’ila ke ba gwamnatin Bahrain gudunmawa wajen murkushe ‘yan adawar siyasa a kasar, da kuma kayan azabtar da su a gidajen kurkuku na kasar.

3557837


captcha