IQNA

23:48 - January 03, 2017
Lambar Labari: 3481096
Bangaren kasa da kasa, gwamnan jahar Sokoto ta rayyar Najeriya ya bayyana cewa za a kara bunkasa a yyukan kur’ani mai tsarki a jaharsa.
Bunkasa Ayyukan Kur’ani A Najeriya

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga jaridar Leadership cewa, Aminu Tambuwal gwamnan jahar Sokoto, ya halarci taron rufe gasar karatun kur’ani mai tsarki ta jahar, wadda ake fiatr da wadanda za su wakilci jahar a gasar kur’ani ta kasa.

A lokacin da yake gabatar jawabinsa a wajen taron gwamnan jahar Sokoto ya bayyana shirinsa na kara bunkasa ayyukan makarantun kur’ani a jahar, inda ya ce an mayar da wasu daga cikin makarantn kur’ani da aka fi sani da makarantun allo zuwa gat sari na zamani.

Ya ce wannan shiri ba yana nufin mayar da su makarntun book ba ne, ana da nufin samar musu da tsari ne na zamani wajen koyar da karatun kur’ani daidai da makarantu na zamani, tare da bayar da tallafi daga bangaren gwamnati ga malami har ma da dalibai na kur’ani.

Gwamnan ya kara da cewa jahar Sokoto ta yi nisa a wajen aiwatar da wanann shiri, wand tuni makarantun kur’ani mai tsarki suka fara cin gajiyarsa a fadin jahar baki daya.

3559223


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: