IQNA

22:15 - January 14, 2017
Lambar Labari: 3481132
Bangaren kasa da kasa, Umar Muhammad Mukhtar Alkadi fitaccen marubuci kuma mai fassarar kur’ani mai tsarki ya rasu.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na almisriyun cewa, Umar Muhammad Mukhtar Alkadi mutumin da ya kwashe tsawon shekaru yana hidim aga kur’ani tare da isar da sakon wannan littafi mai tsarki ga al’ummomin kasashen turai ya rasu.

Ya kasance yana amsa tambayoyin mutane a kasashen yammacin turai dangane da matsalar da suke da ita kan wasu abubuwan da suka shige musu duhu kan kur’ani ko kuma muslunci, inda yake amsa musu tambayoyinsu da kalamai na hankali da ilimi, a kan haka ake yi masa lakabi da jakadan kr’ani a turai.

Haka nan kuma ya kasance mamba na kwamitin bangaren nazarin ilmin kadaita ubangiji da ilimin hankali na cibiyar Azhar, kamar yadda kuma yake amtsayin mamba na jami’oin kasashe daban-daban, hatta cibiyar yada al’adun muslunci ta ISESCO ta zabe shi a matsayin maba a cikin kwamitin jami’ointa.

Alkadi ya karbi shedar karatu ta dokta a cikin shekarar 1984 a jami’ar birnin Paris na kasar faransa, a bangaren nazarin shari’ar muslunci, ya kasance yana jin harsunan turancin ingilishi da kuma Faransanci gami da Italiyanci.

Fitattun mutane a duniya sun aike da sakon ta’aziyarsa da suka hada da Ali Juma’a tsohon mai bayar da fatawa na kasar Masar, da Ibrahim Abu Muhammad babban mai bayar da fatawa na Australia, sai kuma Muhammad Bushara, shugaban kwamitin musulmin kasashen turai.

3562362

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: