Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Babban jojin Amurka neya rantsar da Mista Trump a bikin da akayi yau Juma'a a birnin Washigton.
Bayan rantsardadashi, a cikin jawabinsa Mista Trump ya ce"lokacin fada ba cikawa ya wuce, yanzu lokacin aikatawane''
Hakazalika a cikin jawabin na sa na farko a matsayin shugaban Amurka, Trump ya ce ''Ba zan kara amincewa da 'yan siyasa masu fada ba cikawa ba''
Saidaalkalin kotun kolin Amurka, Clarence Thomas ya rantsar da Mike Pence a matsayin mataimakin shugaban Amurka, kafin daga bisani a rantsarda Mista Trump.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin hada tsohon shugaba Obama da matarsa Michel, sai kuma 'yar takara demokrate data sha kayi a zaben da mai gidanta tsohon shugaba da kuma tsohon shugaba george bush.
Rahotanni daga kasashe daban-daban na duniya suna nuni da cewa dubun dubatan mata ne suka fito kan titunan birane daban-daban na duniya a wani shirin zanga-zanga ta kasa da kasa ta kyamar sabon shugaban Amurka Donald Trump.
Rahotannin sun ce dubun dubatan mata ne ne suka fito a kasashen Birtaniyya, Australia, New Zealand da kuma Japan don gudanar da zanga-zangar kin jinin Shugaban Amurka Donald Trump din.
A Amurkan ma rahotanni sun ce ana sa ran akalla mutane dubu dari biyu za su shiga cikin tattakin da dubban mata suka shirya gudanarwa a birnin Washington don nuna kyamar su ga shugaba Trimp din.
Hakan dai yana zuwa ne kwana guda da rantsar da shi da aka yi a matsayin shugaban Amurka.