IQNA

23:40 - January 24, 2017
Lambar Labari: 3481166
Bangaren kasa da kasa, marigayi sheikh Muhammad Mahdi Sharafuddin daya ne daga cikin fitattun makaranta kuma masu begen manzon da iyalan gidansa, babban burinsa shi ne ziyarar Imam Ridha (AS).

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, a cikin wani file na sautin marigayi sheikh Shafuddin da aka yada a kafofin sada zumunta yana cewa, babban burina shi ne in tafi Mashhad domin ziyarar Imam Ridha (AS).

A cikin wannan sauti yana cewa, Allah ya barnia raye ne ya kuma tsawaita rayuwata domin in ziyarci Imam Ridha (AS), wanda hakan ke nuni da irin tsananin kaunar da wannan bawan Allah yake yi wa iyalan gidan amnzon Allah tsira da amincin Allah su tabata a gare shi da iyalan gidansa tsarakaka, ta yadda ya kasa boye kanar da yake yi walimami na takwas daga limaman ahlul bait Imam Ridha (AS).

Sheikh Sharafuddin dai ya kasance daya daga cikin fitattun masu karatun bege ga manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka a kasar Masar, kuma Allah ya karbi rayuwarsa ajiya Litinin.

Ya kasance yana girmama duk wani lamari da ya shafi kur’ani da kuam makarantan kur’ani mai tsarki, kamar yadda kuma ya zama daya daga cikin wadanda ska bayar da gagarumar gudunmawa ta wannan fuska, duk kuwa da cewa yana da matsalar gani.

Ga wadanda suke son jin karatunsa ko kuma wasu daga cikin wakokin bege, suna shiga wannan link http://www.aparat.com/v/rRDu2 domin ganin hotnansa da kuma jin sautinsa.

3566017

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: