IQNA

Gyaran Makarantun Kur’ani A Kasar Aljeriya

22:23 - February 13, 2017
Lambar Labari: 3481226
Bangaren kasa da kasa, Nuraddin Muhammadi daya daga cikin jami’an ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa nan ba da jimawa za a fara gyaran makarantun kur’ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Al-nahar ta kasar Aljeriya cewa, Nuraddin Muhammadi shugaban bangaren kula da harkokin kur’ani mai tsarkia ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ya bayyana cewa, da yardarm Allah nan a da ‘yan watanni masu zuwa za afara aiwatar da shirin.

Ya ci gaba da cewa wannan shiri an amince da shi tun a cikin shekara ta 1994, kuma ana aiki da shi lokaci zuwa lokaci amma ba amatsayi na kasa baki daya ba, amma daga wannan lokaci shirin zai fara aiki gadan-gadan.

Nuraddini Muhammadi a zantawarsa da jaridar ta Al-nahar ya bayyana cewa; wanann shiri bai takaitu ga gyaran gine-ginen makarantun ba kawai, zai ma hada har da gyaran tsarin manhajar koyarwa, tare da yin sauye-sauye a cikin a cikin salon tsarin koyar da kur’ani a makarantun kasar.

Muhammadi ya yi ishara da irin ci gaba da aka samu a halin yanzu a duniya ta fuskar koyarwa, inda yace akwai hanyoyi da ake amfani da su wajen koyar da wasu ilmomi, wanda kuma za a iya yin amfani da wasu daga cikinsu wajn koyar da kur’ani a cikin sauki ga dalibai a makarantun kasar.

3573898

captcha