Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Echo Press cewa, a jiya an gudanar da wani shiri a jami'ar Alexendria domin amsa tambayoyin mutane da suke da bukatar karin bayanin kan wasu batutuwa da suka shafi kur'ani mai tsarki.
Rashid Firdaus shi ne shugaban kwamitin musulmi na jami'ar, wanda kuma shi ne ya amsa tambayoyin da aka gabatar masa a kan muslunci da kuma mahangar kur'ani kan lamurra da dama da suka shafi rayuwa da siyasa da zamantakewa da sauransu.
Akasarin wadanda suka taru a wurin dai mabiya addinin kirista ne, wasu daga cikinsu sun ukaci jin shin ko kur'ani ya ambaci wani abu dangane da annabi Isa Almasih (AS) da kuma addinin kiristanci.
Rashid ya amsa tambayar da bayani mai gamsarwa, domin kuwa kur'ani mai tsarki ya bayar da muhimmanci matuka dangane da lamarin annabi Isa (AS) da kuma mahaifiyarsa, inda ya ambaci lamarinsu a wurare da da dama a cikin surori da ayoyi daban-daban.
Haka nan kuma annabi Isa yana da matsayi na annabawa na kololuwa a mahangar kur'ani mai tsarki, kamar yadda kuma Maryam take daga cikin mata tsakakaku wadanda Allah ya tsarkake su ya kebance su ya sanya su su zama ayoyi ga dukkanin talikai.
Jawaban da aka bayar kan irin wadannan tambayoyin sun gamsar da mahalrta wurin, inda da dama suka fahimci cewa addinin muslunci addini ne na fahimtar juna ba tashin hankali ko ta'addanci kamar yadda ake ta kokarin bayyana shi ba.
3580583