IQNA

Maulidin Fatima Zahra (SA) A Kasar Senegal

20:44 - March 13, 2017
Lambar Labari: 3481309
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da taron maulidin sayyidah Fatima Zahra (SA) a kasar Senegal wanda ofishin yada al'adun muslunci na Iran zai shirya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci ya bayar da sanarwar cewa, a ranar Laraba mai zuwa za a gudanar da taron maulidin Sayyida Fatima Zahra (AS) a kasar Senegal

Wannan taro dai wanda ofishin cibiyar yada al'adun muslunci ya dauki nauyin shirya tare da wata cibiyar mata a kasar, gami da jami'ar Almustafa zai samu halartar baki daga sassa na kasar.

Daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar dai har da bayanai kan matsayinta da kuma abubuwan da ya kamata aka yi koyi da su a cikinsu rayuwarta mai albarka, musamman ma ga mata.

Baya ga mutanen kasar ta Senegal, Iraniyawa mazauna kasar da kuma 'yan kasar Lebanon duk za su halarta, domin raya wanann taro mai albarka na tunawa da maulidin diyar manzon Allah tsira da amincin Alllah su tabbata agare shi.

3583550
captcha