IQNA

23:41 - March 29, 2017
Lambar Labari: 3481356
Bangaren kasa da kasa mahukuntan kasar Saudiyya sun kasha 'ya'yan ammin shahid Sheikh Nimr su biyu a yankin Ramis da ke cikin gundumar Alawamiyya a gabashin saudiyyah.

BKamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jami'an tsaron masarautar 'ya'yan Saud sun kaddamar da farmakia a gudanar dangin Sheikh Nimr inda suke gudanar da ayyukansu na noman rani

A yayin wannan farmaki sun kashe Muhammad da muma Miqdad Nimr, wadanda dukakninsu 'ya'yan ammin sheikh Nimr ne da masarautar ta kasha shekarar da ta gabata.

Babu wani dalili da masarautar iyalan gidan Saud ta bayar kan aikata wannan mummunan aiki na kisan kai a kan 'yan kasa masu cikakken hakkin kamar kowane dan kasa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jami'an tsaron wannanmasarauta suke kaddamar da hari kan fararen hula a yankunan gabashin kasar Saudiyya ba, wadanda yankuna ne na mabiya mazhabar shi'a, wadanda su ne kimanin kashi goma sha biyar na al'ummar kasar baki daya.

Wannan masarauta dai tana kallon mabiya mazhabar shi'a a kasar tamkar ba 'yan kasa ba, domin kuwa ana haramta musu dukkanin hakkokinsu wadanda babu wata doka da ta haramta musu, bil hasali ma dukkanin albarkatun man fetur da iskar gas da tattalin arzikin kasar ya dogara a kansu, ana fitar da su ne daga yankunan mabiya mazhabar shi'a da ke gabashin kasar ta Saudiyya.

Kiran da sheikh Nimr yake yi ga mahukuntan wannan kasa da su ji tsoron Allah, su baiwa kowane dan kasa hakkinsu daga hakkokinsa da dokar kasa ta ba shi, shi ne babban abin da ya harzuka mahukuntan masarautar 'ya'yan Saud suka sare masa kai, kamar yadda suke a kan duk wanda ya taba mulkinsu.

3586044
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: