Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na mauid cewa, an kaddamar da kwamitin kula da harkokin da suka shafi abubuwan ci na halal a kasar Aljeriya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kwamiti zai dauki nauyin sanya idoa kan dukkanin lamurra da suka shafi abincin halal da ake shigowa da shi daga kasashen ketare, tare da tabbatar da ingancinsa.
Kasar Aljeriya a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu girma a cikin kasashen msuulmi, za ta mayar da hankali matuka wajen samar da abubuwa na halal da kuma shigo da su daga waje domin fadada mu'amala tsakanin kamfanoninta da na kasashen musulmi a wannan fage.
A zaman kaddamar da wannan kwamiti an samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma malamai gami da masana da kuma shugabannin kamfanoni gami da 'yan kasuwa.
'Yanzu haka dai akwai wuraren gwaji kimanin 2000 a kasar ta Aljeriya wadanda za su yi aki wajen wajen tantance abincin da ake shigowa da shin a halal kafin bayar da damar sayar da shi ga al'ummar kasar.
3586512