Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na izia.at cewa, a ranar 13 ga watan rajab za a gudanar da taron maulidin Iamm Ali (AS) a babbar cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna na kasar Austria.
Wannan taro kamar yadda aka saba ana gudanar da laccoci ga mahalarta, dangane da matsayin Imam Ali (AS) da kuma irin muhimman abubuwan da ya kamata dukaknin msuulmi su koyi da su a cikin rayuwarsa mai albarka.
Taron dai yana daga cikin manyan taruka da wannan cibiya ta saba gudanarwa, kuma daruruwan musulmi suna halarta domin sauraren jawaban da ake gudanarwa.
Daga cikin amsu halartar wanann wuri akwai musulmi daga kasashen larabawa da kuma Iraniyawa mazauna kasar ta Austria.