IQNA

Vatican Ta Ce paparoma Zai Yi Tafiya Zuwa Masar

22:47 - April 11, 2017
Lambar Labari: 3481396
Bangaren kasa da kasa, fadar Vatican ta sanar da cewa, duk da hare-haren da aka kai a kan majami’oin mabiya addinin kirista a kasar Masar, tafiyar Paparoma Francis zuwa Masar na nan darama cikin wannan wata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Al-shuruq ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, Fadi Francis daya daga cikin mambobin kwamitin tsara tafiye-tafiyen Paparoma a fadar Vatican ya sheda cewa, tafiyar Paparoma zuwa Masar na nan kamar yadda aka tsara.

Fadi Francis ya ce babu gaskiya a cikin rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka yada, da ke cewa Paparoma ya dakatar da tafiyarsa zuwa kasar Masar, sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai a kan manyan majami’iun mabiya addinin kirista a kasar.

A ranar 27 ga wannan wata na Afrilu ne dai paparoma Francis zai kai ziyara ta kwanaki biyu a kasar Masar, inda zai gana da shugaban kasar Abdulfattah Sisi, da kuma babban jagoran mabiya addinin kirista na kasar, gami da babban malamin cibiyar Azhar.

3588807


captcha