Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a zaman da kwamitin kula da harkokin addinin muslunci na majalisar dokokin kasar Masar ya gudanar a jiya a karkashin jagorancin Usama alabd, ya buklaci a kara yawan kasafin kudaden da ake warewa domin harkokin kur’ania kasar.
Kwamitin ya ce a bana an ware pan miliyan 66 maimakon miliyan 62 da ake warewa kan ayyukan masallatai da harkokin kur’ani da suka hada da shirya gasa da sauransu, amma duk da hakan wadannan kudade ba za su isa ba, idan aka yi la’akari d matsayin kasar da kuma yadda take it ace ta daya aduniya tafuskar karatun kur’ani da da sauran lamurra da suka danganci haka.
Kwamitin ya ce zai mika wannan bukata ga zaman da za a gudanar domin duba kasafin kudaden da za a kashe a kasara tsakanin shekaru 2017 – 2018 mai zuwa.