Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, an fara gudanar da shirin raba kur’anai sabbi fiye da dubu 6 a yankin kakamga da ke yammacin kasar Kenya, domin maye gurbin tsoffin kur’anai da sabbi a cikin wannan wata mai alfarma.
Bayanin ya ce yanzu haka dai kimanin masallatai da cibiyoyin addinin muslunci 182 ne za su ci gajiyar wannan shiri.
Sheikh Hussain sama shi ne shugaban cibiyar yada addinin musluinci ta kasar Kenya ya bayyana cewa, bababr manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa an shigar da kur’anai a dukkanin lunguna na wannan yanki mai yawan musulmi, kuma shirin zai fishafar kauyka ne, domin kuwa su ne bas u cika samun sabbin kur’anai ba.