Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, babbar jami'a mai kula da harkokin wajen tarayyar turai Federica Mogherini ta yi tir da Allah wadai da harin da aka kai a birnin Tehran tare da bayyana hakn a matsayin aiki ne na ta'addanci mai sosa rai.
Ta ce hakika abin da ya faru ya sanya ranar yau ta zama ranar bakin ciki, kuma tana ci gaba da bin kadun abin da yake faruwa dangane da harin na Tehran, kuma za ta ci gaba da tuntubar ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jawad Zarif a kan batun.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Amurka Richard Haas ya bayyana cewa, ya zama wajibi a yi Allah wadai da wannan hari, ba zai yiwu a kai hari a wata kasa ba Amurka ta yi Allah wadai amma an kai harin ta'addanci tare da kasha mutane a Iran a shiru ba.
Ya ce yana kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya fito ya yi tir da Allah wadai da wannan hari da aka kai a birnin Tehran a yau.
Ya ce dole ne shugaban Amurka ya san cewa babu banbanci a kan harin ta'addanci a kasashen turai koa Iran.