Kamfanin dillanicn labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai a kan jama'a ayau a majalisar dokokin Iran da kuma hubbaren Imam Khomeini (RA) ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiya ta mika sakon ta'aziyya ga Iran da kuma iyalan dukkanin wadanda abin ya shafa.
Shi ma kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya a safiyar yau ya yi shiru na minti guda don tunawa da Iraniyawan da suka rasa rayukansu a hare haren ta'addancin guda biyu da aka kai a nan birnin Tehran.
Kasashen duniya da dama suna ci gaba da mika sakon ta'aziyyarsu ga al'ummar Iran, tare da nuna alhini kan abin da ya faru da kuma yin Allawadai da duk wani aikin ta'addanci.