Lamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na albawabhnews cewa, an fara gudanar da wannan gasa wadda takebanci ma’aikatan cibiyar azhar zalla a karkashin kulawar babban malmin ciyar tare da wakilcin Abbas Shauman.
Wannan gasa dai tana daga cikin irin ta ake gudanarwa a kowace shekara a cikin watan Ramadan, inda tun farkon watan aka sanar da cewa wadanda suke da bukata za su iya gabatar da sunayensu.
Gasar dai ta kebanci bangarori hudu ne, hardar dukkanin kur’ani da tajwidi, kashi uku bisa hudu na kur’a da tajwidi, rabin kr’ani da tajwidi, sai kuma kwata na kur’ani da tajwidi.
Ana gudanar da gasar ne a rana guda kawai a tsakiyar watan Ramadan, idan an kammala kuma sai wata shekara ta gaba.