IQNA

Azumin Watan Ramadan A Iran A Talabijin Na Aljeriya

23:41 - June 12, 2017
Lambar Labari: 3481603
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani shiri kan yadda ake gudanar da azumin watan Ramadan a kasar Iran a wata tashar talabijin ta Alshuruq a kasar Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hula da jama’a na cibiyar yada aladun muslunci cewa, a jiya tashar Alshuruq ta Aljeriya ta nuna wani fim kan yadda ake gudanar da zumin watan Ramadan mai alfarma akasar Iran.

A cikin fim dinan zanta da jakadan kasar Iran a kasar ta Aljeriya da kuma Sayyid Abdulamir Musawi Badr shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na kasar Iran a kasar.

Baya ga haka kuma tashar ta nuna yadda al’ummar Iran suke dukufa wajen gudanar da wasu ayyuka na musamman a cikin wannan wata mai albarka, da hakan ya hada da tarukan karatun kur’ani a manyan masallatai da cibiyoyon addini, da kuma yadda jama’a suke gudanar da wasu al’adu na musamman a wannan lokaci.

Daga cikin irin aladun har da yin wasu nauin abinci wadanda suka kebanci watan Ramadan kawai, da kuma yadda ake gudanar da buda baki a masallatai da cibiyoyin addini tare da halartar dubban mutane.

Baya ga haka kuma shirin ya tabo yadda ake gudanar da taruka da kuma jerin gwano na ranar Qods ta duniya wadda marigayi Imam Khomeini (RA) ya ayyana a jumar karshen kowane watan Ramadan.

Haka nan kuma tashar ta tabo batun ziyarar Trump a Saudiyya da kuma yadda sarakunan wannan kasa suka kaskantar da kansu a gaban diyar Trump.

3609086


captcha