IQNA

Yanayin Watan Ramadan A Kasar Togo

20:23 - June 13, 2017
Lambar Labari: 3481606
Bangaren kasa da kasa, a lokacin azumin watan ramaan mai alfarma musulmin kasar Togo suna gudanar da harkokinsu na addini fiye da sauran watanni da ban a Ramadan ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Saraya cewa, atun daga farkon watan watan Ramadan musulmi a kasar Togo suna fara gudanar da wasu aikace-aikace na musamman da suka kebanci wanann wata.

Daga cikin abubuwan da ake gudanarwa akwai tarukan karatun kur'ani da kuma tafsiri, wanda malamai suke gudanarwa, baya ga haka kuma akwai gasar harda da karatun kurani da ake gudanarwa asassa daban-daban na kasar inda msuulmi suke rayuwa.

Haka nan kuma iyaye suna kokarin ganin yaransu sun halarci wuraren taruka na addini, kamar yadda kuma suke jan hankalinsu zuwa masallaci domin yin salla ko kuma sauraren tafsirin kur'ani mai tsarki.

Tun daga lokacin da yara suka fara tasowa ake basu tabiya ta yin azumi, inda sukan saba da azumi tun kafin su kai shekarun balaga, saboda haka a lokacin da taklifi yah au kansu sun saba da ibada.

Masallacin birnin Lome fadar mulkin kasar na daga cikin msallatan da suka fi cika a lokacin azumin watan Ramadan, inda ake gudanar da harkokin addini a cikinsa, baya ga salla ana gudanar da karatun kur'ani da kuma fadakarwa da malamai ke yi ga musulmi.

Musulmin kasr Togo dai su ne marassa rinjaye, inda suke a matsayin kashi daya bisa uku na dukanin alummar kasar, duk da cewa su ne marassa rinjay, amma kuma suna samun kulawa da kare hakkokinsu yadda ya kamata daga mahukuntan kasar.

3601771


captcha