Ya gabatar da karatun kur'ani a daren 27 na watan Radan wanda shi ma ake lissafa shi a cikin dararen lailatun Qadr a wajen wasu malamai, karatun ya guda ne a masallacin Hassan na biyu tare da halartar sarki Muhammad na shida.
Karatun ya dauki hankulan dukaknin mutanen da suke a wurin, kasantuwar ya shahra wajen kiyaye kaidoji na tajwidi da karatun kur'ani mai tsarki.
Wannan yaro dai yana aji na biyu ne a hain yanzu makarantar gabada firamare, kuma si ne ya zo na biyu a gasar karatun kur'ani ta duniya a a birnin Dubai a cikin shekara ta 2013.
An haifi Zubair Algauri ne a garin Kazablanka shekaru 13 da suka gabata, kuma ya yi karatun kur'ani a garin tare da taimakon mahaifansa, inda a halin yanzu shi ne yarin da aka zaba a matsayin yaron da ya fi kowa ta fuskar karatun kur'ani a cikin kasashen larabawa, kuma ya samu kyautar sarki Muhammad na shida.
Karamin Yaro Ya Yi Karatun Kur'ani A Gaban Sarkin Morocco