Kamfanin dillancin labaran iqna ya
bayar da rahoton cewa, kamfanin dilalncin labaran Saumaria News daga Iraki ya
bayar da rahoton cewa, a wannan Talata Kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar da
wani kajeran labari inda a cikin sa ta tabbatar da mutuwar Shugabanta Abubakar
Bagadadi tare da cewa nan gaba za ta sanar da sabon Khalifanta.
Kafar watsa labaran ta ce kwanaki biyu da suka gabata, cikin wani sako da fitar a shafinta na Intagram kungiyar ta ISIS ta haramta watsa duk wani labari da ya shafi mutuwar Shugaban Kungiyar Abubakar Bagdadi, domin hakan ne ma masu sharhi ke ganin cewa wannan shi ne dalilin da ya sanya kungiyar ta ISIS ta gaggauta tabbatar da mutuwar ta Bagdadi.
Tun ranar sha shiga ga watan Yuni da ya gabata rasha ta sanar da cewa ta halaka shi a kusa da garin Raqqah, a yau kuma kungiyar 'yan ta'addan ta ISIS ta tabbatar da halakar tasa.