Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin Arab 48 ya bayar da rahoton cewa, aa'a yin Sallar a cikin zaman dar-dar kasancewar ko a jiya Alhamis an yi dauki ba dadi tsakanin Palasdinawa da kuma jami'an tsaro yahudawan mamaya na Isra'ila, inda dariruwan mutane suka jikatta.
Palasdinawa dai sun daina sallah a harabar masallacin na Baitul Mukaddas domin kalubalantar matakan tsaron Isra'ila a masallacin.
A jiyane dai Isra'ila ta kammala kwashe na'uroringano karafan data kafa a masallacin.
Matakin janye na’urorin daga Masallacin na birnin Kudus na zuwa ne bayan da kasashen duniya sukabukaci kawo karshen rikicin, wanda su ka yi gargadin cewa, kan iya kaiwa har inda ba'a tsammani.