Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, Hadi Amiri ya bayyana cewa, dakarun Iraki da kuma sauran dakarun sa kai
na al'ummar Iraki suna ci gaba da yi garin Tal Afar kawanya, wanda yake
ahannun 'yan ta'addan na IS, ya ce adadin dukkanin 'yan ta'addan da ke cikin
garin bai wuce 1600 zuwa 2000 ba.
Ya ce yanzu haka sun fara kwace iko da wasu unguwanni da suke gefen birnin, wanda hakan zai ba su damar ci gaba da nausawa zuwa cikin birnin, kuma cewarsa yaki da 'yan ta'addan domin tsarkake Tal Afar ba zai dauki wani dogon lokaci ba.
A jiya ne dakarun Iraki suka fara kaddamar da farmakin tsarkake birnin tal Afar daga 'yan ta'addan takfiriyya na Daesh, da ke samun dauki daga wasu gwamnatocin kasashen kasashen larabawa.