Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da
rahoton cewa, tashar talabijin ta almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a
lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya, babban sakataren kungiyar
Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu tun bayan fara
kaddamar da farmaki na hadin gwiwa tsakanin sojojin Syria da mayakan Hizbullah
a yankunan da ke iyakar Syria da Lebanon, an samu gagarumar nasara a kan 'yan
ta'addan takfiriyya na Deash.
Sayyid Nasrullah ya kara da cewa, akwai kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin dakarun Lebanon da na Syria da kuma Hizbullah wajen kaddamar da wannan farmaki, inda dakarun Lebanon suke gudanar da nasu a ikin a cikin yankunan Arsal, yayin da sojojin Syria da dakarun Hizbullah suke mayar da hankali a gundumar Qalamun ta yamma.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, a daidai lokacin da ake fatattakar 'yan ta'addan, ana bin salon da aka yi amfani da shi wajen fitar da 'yan ta'addan jabhat Nusra daga yankunan da ta kame a lokutan baya a cikin Lebanon.
A karshen jawabin nasa Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, 'yan ta'addan Daesh sun yi rauni matuka, kuma za a kawo karshenta da izinin Allah.