Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar kasar Saudiyya ta Ukkaz cewa, an fara gudanar da gasar kur’ani ta kasar baki daya akaro na biyu a kasar Sudan, wanda wasu bangarori na kasa da kasa suke daukar nauyin wannan gasa.
Gasar dai tana samun halartar mahardata kimanin 200 daga dukkanin larduna na kasar, wadanda suke karawa da juna a cikin gasar a dukkanin matakai.
Gasar tana bangarori uku, da suka hada da bangare na farko shi ne hardar juzui 20, sa kuma juzui 10 da kuma kasa da hakan, wanda dukkanin bangaren da mai gasa yake zai kara da takwarorinsa a cikin rukunin da yake.
Hamid Bin Aiq Rufai shi ne babban daraktan cibiyar bayar da agajin gagawa ta kasar, ya bayyana cewa wannan gasa tana da nufin kara bunkasa ayyukan jin kai da taimakon al’umma akasar baki daya.
Ya ce a shekarar da ta gabata ce aka fara gudanar da ita, kuma ta samu karbuwa matuka daga dukkanin al’ummar kasar, inda kungiyoyin bayar da agaji na kasashen musulmi suke Dakar nauyin gasar tare da gudanar da ayyuka na musamman a kasar.