IQNA

Alhazan Bana Adadinsu Ya Haura Na Bara

23:53 - August 29, 2017
Lambar Labari: 3481844
Bangaren kasa da kasa, Mahukuntan kasar saudiyya sun ce adadin mahajjatan bana ya karu da kusan maniyyata rabin miliyan, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na elbashayeronline.com ya bayar da rahoton cewa, babban jami'in hukumar shige ta fice ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa, ya zuwa adadin alhazan da suka isa kasar Saudiyya ya kai mutane miliyan daya da dubu 730, wanda hakan ke nuni da cewa adadin ya karu da mutane fiye da dubu 412 ida aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ya kara da cewa yanzu haka dai an mayar da wasu maniyyata 18 da suka iso kasar ta Saudiyya zuwa kasashensu, saboda sun shigo kasar ba tare da cikakkun takardun izinin shigowa kasar ba.

Tun daga fara shirye-shiryen aikin hajjin bana, maniyyata da dama sun rasa rayukansu sakamakon rashin lafiya da wasu matsaloli na daban a Jidda da kuma Madina dama birnin makka mai alfarma.

3635775


captcha