A cikin hudubar sallar idin an yi addu’a ga wadanda suka yi shahada daga cikin sojojin kasar da kuma dakarun sa kai, da kuma yin addu’a ga wadanda suka samu raunuka daga cikinsu, kamar yadda mai hudubar ya jinjina muus a kan nasarar da aka samu a kan ‘yan ta’adda.
Bisa fatawar da Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayar,a yau ne ranar idin babban salla a kaar Iraki, wanda kuma wasu daga cikin malaman kasar sun tafi a kan hakan, yayin da kuma wasu suka sanar da jiya a matsayin ranar idin babban salla.