Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alghadir cewa, tun daga daren jiya aka fara gudanar da tarukan Ghadir a hubbaren Imam Ali (AS) har zuwa yau.
Wannan taro ya samu halartar dubban daruruwan jama’a daga dukkanin sassa na kasar Iraki, wadanda suka ziyarci Imam Ali (AS) a hubbarensa tare da raya wadannan taruka masu albarka da aka gudanar.
Haka na kuma an gudanar da wasu tarukan makamantan wannan a sassa daban-daban na kasar ta Iraki, musamman a hubbarorin limaman iyalan gidan manzon Allah (SWA) da kuma masallatai gami da husainiyoyi da cibiyoyin addini.
Baya ga haka kuma an gabatar da jawabai a dukkanin wuraren gudanar da wadannan taruka masu albarka, dangane da wannan rana da kuma matsayinta acikin addinin muslunci, ranar da Allah madaukakin sarki ya cika addininsa.
A dukkanin wuraren da aka gudanar da wadannan taruka musamman a birnin Najaf da kuma wasu hubbarorin limaman iyalan gidan manzon Allah masu tsarki da suke a wasu birane na kasar ta Iraki.