Kamfanin dillacin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta Nes cwa, a yau miliyoyin muminai sun hadu a birnin Karbala domin gudanar da tarukan ashura.
A yayin taron nay au ana gudanar da makoki na tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) da kuma dan uwansa Abbas (AS) da sauran iyalan gidan manzon Allah da kuma sahabban Imam wadanda suka kasance tare da shi a wurin.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar a yau har da sassarfa tsakanin hubbarori biyu masu albarka na Imam Hussain (AS) da kuma Abbas (AS) da ke ta zara ta mitoci kamar 20 a tsakaninsu.
Tun a cikin shekara ta 1885 ake gudanar da wannan taro a hukumance kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da shi, duk kua da yunkurin da wahabiyawa suka yin a ganin sun kawo cikas ga wannan taro mai albarka a lokacin da suka kaiwa Iraki hari.