IQNA

Masana A Afirka Na Goyon Bayan Palastine

22:14 - October 09, 2017
Lambar Labari: 3481983
Bangaren kasa da kasa, a wani taron da masana da malaman addini suka gudanar a birnin Capetown na kasar Afirka ta kudu sun nuna goyon baya ga Palastine.
Masana A Afirka Na Goyon Bayan PalastineKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Sabah cewa, wannan taro ya hada masana daga ciki da wajen kasar.

Baya ga batun Palastinu, an tabo batutuwa da suka halin da musulmi suke cikia kasashen Syria, Myanmar, Yemen da Afghanistan, da kuma tunanin samo hanyoyin taimaka masu da fitar da su daga halin da suke ciki.

Abdulrahman Iskandar shi ne shugaban masallacin quds na kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, wannan taro yan ada matukar muhimamnci dangane da samun hanyoyin taimaka ma musulmi da suke fuskantar matsaloli.

Babbar manufar taron dai ita ce tattauna batun Palastine, a gefen haka kuma na tattauna sauran batutuwa na kasashen msuulmi, taron ya samu haartar masana 400 daga sassa na kasar da wasu kasashe.

3650766


captcha