Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan makala tana magana ne a kan matsayin Ashura a kasar ta Senegal wadda take da yawan mabiya addinin muslunci masu kaunar ‘ya’yan manzo.
Saud Lee dalibar jami’a ce da take karatun digirin digirgir a jami’a a kasar ta Senegal, kuma ta yi kokari a cikin makalar ta bayyana yadda ake gudanar da tarukan Ashura a kasar Iran.
Daga cikin abubuwan da ta yi ishara da su har da tarukan da ake gudanarwa a wannan rana, da suka hada gabatar da jawabai kan matsayin iyalan gidan manzon Allah, da kuma yin makoki kana bin da ya faru da na kuntatawa.
Ta ce a kasar Senegal ana yin taro makamacin wannan wanda yake farawa daga ranar 18 ga watan safar ranar da aa kori sheikh Ahmadu Bamba, daya daga cikin waliyai da ae girmama a kasar, inda mutane sukan yi tafiya a kasa har zuwa hubbarensa, wanda ya zo daidai da lokacin gudanar da tarukan ziyarar arbaeen na Ashura.