Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa mahukuntan kasar Saudiyya ne suka tilasta Saad Hariri yin murabus kuma suke ci gaba da tsare shi tare da hana shi komawa kasar Lebanon.
A jawabin da ya gabatar a yau Juma'a a zaman taron juyayin cikan ranaku arba'in na jikan manzon Allah Imam Husani {a.s} kuma ranar tunawa da shahidan kungiyar Hizbullahi ta Lebanon: Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewa A halin yanzu dukkanin al'ummar Lebanon da ma duniya sun kai ga tabbacin cewa Mahukuntan Saudiyya suna tsare ne da Sa'ad Hariri kuma tilasta masa suka yi kan yin murabus daga kan mukaminsa na fira ministan Lebanon. Kamar yadda suke son gabatar da wani mutum na daban a matsayin sabon fira ministan kasar.
Har ila yau Sayyid Hasan Nasrullahi ya fayyace cewa Murabus din Sa'ad Hariri kan mukaminsa na fira ministan Lebanon baya kan doka domin tilasta masa aka yi, sakamakon haka al'ummar Lebanon suna daukansa a matsayin fira ministan kasarsu mai halacci.
Sayyid Hasan Nasrullahi ya kara da cewa: A yau ta bayyana a fili cewa: mahukuntan Saudiyya suna shirya makirce-makirce kan kasar Lebanon tare da kunna wutan yaki kan kasar, kamar yadda suke kokarin zaburar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Lebanon. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullahi ya kuma fayyace cewa: Yakin wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan kasar Lebanon a shekara ta 2006, yaki ne da ta kaddamar bisa bukatar masarautar Saudiyya.
Jawabin na babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya kuma tabo batun irin makirce-makircen da masarautar Saudiyya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suke kitsawa kan kasar Lebanon musamman bayan da mummunan shirinsu na kunna wutan rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda musamman kungiyar Da'ish ya kasa cimma nasara.
Hakika dalilai da hujjoji kwarara sun tabbatar da irin rawar da mahukuntan Saudiyya suka taka a fagen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Lebanon a shekara ta 2006, Amos Yadlin tsohon janar a rundunar sojin saman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, kuma shugaban cibiyar leken asirin rundunar sojin kasar a halin yanzu, ya yi furuci da cewa: A hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar kan kasar Lebanon na tsawon kwanaki 33 a shekara ta 2006, sun samu bayanai masu muhimmanci daga mahukuntan Saudiyya. Har ila yau Jaridar The Times ta kasar Birtaniya a watan Yunin shekara ta 2010 ta watsa labarin cewa: Mahukuntan Saudiyya sun bada izini kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi amfani da sararin samaniyarsu wajen kaddamar da hare-hare kan kasar Lebanon da nufin rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi.
Sakamakon haka a fili yake cewa babbar manufar masarautar Saudiyya da masu goya musu baya musamman haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce kokarin kunna wutan rikici a kasar Lebanon da zai rikide zuwa yakin basasa da nufin samun damar rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi domin samun saukin shimfida bakar aniyarsu a kasar da ma yankin baki daya.