Wannan dais hi ne karo na biyu da ake gudanar da wannan gasar kur'ani ta kasa da kasa da ta kebance mata zalla a Dubai, inda yanzu haka wakilai 75 ne daga kasashen duniya daban-daban suke halartar wannan gasa.
A ranar farko Zainab Ali Gidan Kano daga Najeriya, Bibi Hajar daga Pakistan, Nura Muhammad Ahmad daga Amurka, Ala Azmal Jamil daga Maldev, Nadiya Said Ahmad daga Norway, Khadijah Ishaq Abdulrahim daga Chad, su ne suka kara da juna.
Abin tuni a nan dai shi ne, mahardaciyar kur'ani Zahra Sadat Husaini 'yar shekaru 10 daga lardin Khorasan it ace take wakiltar Iran a wannan gasa.
Hanah Khalfi ita wata karamar yarinya maishekaru kasa da goma, ita ce ta waklici Iran a shekarar da ta gabata a wannan gasa.