Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a ci gaba da gudanar da tarukan maldin manzon Allah (SAW) a birane daan-daban na kasar Senegal al’ummar musulmi masoya manzon Alah suna ci gaba da kara bayar da himma wajen raya wadannan ranau masu albaka.
A birnin TIVAOUANE daya daga cikin manyan birane na mabiya darikar Tijjaniya a kasar Senegal, an gudanar da wani gagarumin taron maulidin manzon Allah tare da halartar wasu jami’ai daga kasar Iran, da suka hada da shugaban karamin ofishin jakadacin kasar Sayyid Hassan Ismati.
Kasashen Iran da Senegal suna da kyakyawar alaka ta fuskar al’adu da kuma ilimi, kasantuwar kasashen biy sun yi tarayya a kan muslunci da kuma bin tafarkin son iyalan gidan manzon Allah da waliyan Allah.
Kasar Iran ta bayar da taimako ga zawiyoy daban-daban na mabiya dariku a kasar Seegal domin shirya tarukan maulidin manzon Allah (SAW).