IQNA

Gasar Kur'ani Ta 'Yan Mata A Kasar Libya

22:47 - February 07, 2018
Lambar Labari: 3482373
Bnagaren kasa da kasa, cibiyar Fatima Zahra da ke garin Tubruk na kasar Libya ta shirya gasar hardar kur'ani mai tsarki ta 'yan mata zalla.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alwasat ya habarta cewa, wannan cibiyar ta shirya wannan gasar ne a fagen harda.

Wannan gasar kur'ani an shirya ta ne domin 'yan mata wata suke karatu a makarantun firamare da kuma sakandare, inda Nusaiba bint ka'ab tare da wasu masu koyar da ilimin kur'ani ne suka jagoranci gasar.

Haka nan kuma an gudanar da gasar an gudanar da ita ne a juzui na biyar da kuma uku da biyu, daga karshe kuma nan girmama wadanda suka nuna kwazo a mataki na daya zuwa na uku.

Cibiyar Fatima Zahra tana gudanar da ayyukanta ne a garin Tubruk a kasar Libya, kuma ayyukanta suna tasiri matuka wajen ci gaban 'ya'yan mata a wajen harkokin kur'ani mai tsarki, ta fuskar karatu da kuma harda.

Garin Tabruk dai yana daga arewacin kasar Libya ne inda aka gwamnai da ke tafiyar da kasar kafin cimma yarjejeniyar hadin kan kasa wadda ta hada mahukuntan Tripoli da kuma na yankin.

3689394

 

 

 

 

 

 

captcha